1 Afirilu 2020 - 10:18
Najeriya : Gwamnati Ta Sake Rage Farashin Mai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da sake rage farashin man fetur zuwa naira 123 da kwabo 50 a duk lita.

(ABNA24.com) Za a fara amfani da sabon farashin ne daga yau 1 ga watan Aprilu, kamar yadda babban jami'i a sashen kula da albarkatun mai da kayyade farashin mai na kasar Abdulkadir Sa'idu, ya sanar a cikin wata sanarwa.

A cewar sanarwar, an rage farashin ne bisa la'akari da yadda farashin danyen mai ya fadi a kasuwannin duniya sakamakon cutar coronavirus.

Wannan shi ne karo na biyu a kasa da wata guda da gwamnatin Najeriyar ke rage farashin lita na man fetur a kasar, inda ko a ranar 19 ga watan Maris din nan da mukayi ban kwana da shi 2020, gwamnati ta rage farashin man fetur daga naira 145 zuwa naira 125.

Farashin danyen man fetur ya yi mummunar faduwar da bai taba yin irinta ba cikin shekaru da dama a kasuwannin duniya, sakamakon annobar coronavirus da kuma sabanin dake tsakanin kasashen Saudiyya da Rasha kan yawan man da suke fitarwa.

342